Wikipidiya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Wikipidiya Insakulofidiya ce ta kyauta da ke tattare da harsuna daban-daban a fadin duniya, wanda al'ummomi masu bada gudummawa ke rubuta mukalai ta hanyar hadin gwiwa a fili (ba tare da ɓoye-ɓoye ba). A turance a na kiran editocinta da suna Wikipedians. Wikipidiya ta kasance farfajiyar nazari mafi girma a tarihin ilimin duniya.[1] Ta kasance daya daga cikin fitattun shafukan yanar gizo guda goma a duniya kamar yadda Similarweb ta zayyano; i zuwa shekara ta 2022 kuwa, Wikipidiya itace ta 7 a cikin jerin fitattun shafuka na yanar gizo a duniya.[2][3][4] gidauniyar Wikimedia Foundation ce ke daukan nauyin shafin wikipidiya. ita kuwa Wikimedia Foundation wata kungiya ce wanda ba'a samar da riba (wato non-profit organization a Turance) na kasar Amurka, kuma suna samun kudadensu ne ta hanyar taimako/gudummawa (donation) daga wasu kungiyoyi ko jama'a.[5]
File:Wikipedia Portal Screenshot (2022).svg da Wikipedia pagina principal.png | |
URL (en) | https://wikipedia.org/ |
---|---|
Eponym (en) | Wiki da Insakulofidiya |
Gajeren suna | Wikipédia, Wikipedia, ウィキペディア, Viquipèdia, Wikipèdia, Vicipaedia, Wikipedia, Βικιπαίδεια, ဝီကီပီးဒီးယား, ويكبيديا da Wikipedia |
Iri | online encyclopedia (en) , MediaWiki website (en) , Wikimedia Foundation project (en) , open content (en) , crowdsourced project (en) , self-depicting entity (en) , specialty (en) , user-generated content platform (en) da very large online platform (en) |
Slogan (en) | the free encyclopedia that anyone can edit, الموسوعة الحرة التي يستطيع الجميع تحريرها, vapaa tietosanakirja, de vrije encyclopedie, свободная энциклопедия, которую может редактировать каждый, Die freie Enzyklopädie, 人人可编辑的自由百科全书, 人人可編輯的自由百科全書, একটি উন্মুক্ত বিশ্বকোষ, যা সবাই সম্পাদনা করতে পারে, ウィキペディアは誰でも編集できるフリー百科事典です, L'enciclopèdia de contingut lliure que tothom pot millorar, Төрлө телдә яҙылған, сикләүһеҙ ҡулланыуҙа булған ирекле интернет энциклопедия. Һәр кем уны төҙөүҙә ҡатнаша ала., آزاد دائرۃ المعارف جس میں کوئی بھی ترمیم کر سکتا ہے, La enciclopedia de contenido libre que todos pueden editar., A szabad enciklopédia, Ազատ հանրագիտարան, որը կարող է խմբագրել յուրաքանչյուր ոք:, האנציקלופדיה החופשית שכולם יכולים לערוך, Wolna encyklopedia, którą każdy może redagować, 海納百川,有容乃大 da La libera enciklopedio redaktebla de ĉiuj. |
Language (en) | multiple languages (en) |
License (en) | Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International (en) da Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 Unported (en) |
Programming language (en) | PHP (en) |
Software engine (en) | MediaWiki (en) |
OCLC, Inc. (en) | 52075003 |
Mai-iko | Wikimedia Foundation da Jimmy Wales |
Maƙirƙiri | Jimmy Wales, Larry Sanger da Wikimedia community (en) |
Mai wallafawa | Al'ummar Wikipedia |
Web developer (en) | Jimmy Wales da Larry Sanger |
Service entry (en) | 15 ga Janairu, 2001 |
Wurin hedkwatar | Tarayyar Amurka |
Kyauta ta samu | Princess of Asturias Award for International Cooperation (en) , FSF Free Software Award for Projects of Social Benefit (en) , Grimme Online Award (en) da Erasmus Prize (en) |
Alexa rank (en) |
13 (4 Nuwamba, 2020) 5 (31 Oktoba 2017) 5 (7 Nuwamba, 2017) 5 (20 Nuwamba, 2017) 9 (2 Oktoba 2019) 10 (1 ga Faburairu, 2020) 14 (ga Augusta, 2020) 7 (4 ga Afirilu, 2009) 13 (18 Disamba 2020) |
Wikipedia | |
Wikipedia | |
wikipedia |
Wikipedia shafi ne na yanar gizo wanda masu bada gudummawa ke rubuta mukalai kuma su ke gudanar da ita, ta hanyar shigar da ilimi ko gyare-gyare da sauransu. Ana kuma kiran duk wani mai gyare-gyare ko shigar da ilimi a shafukan Wikipedia da suna "Wikipedian". Wikipidiya tana tattare da harsunan duniya da dama, a shafinta kowa na iya ƙirƙira ko gyara muƙala a kyauta domin taimakawa wajen samar da ilimi kyauta, wannan ne yasa wikipidiya tayi zarra a duk duniya wurin samar da ilimi daga asalin inda ilimin ya fito.
Kowa da kowa na da damar bada gudummawa wajen yada ilimi ta hanyar ƙirƙiran sabuwar muƙala ko gyara ƙirƙirarrun muƙalai da ke buƙatan a ingantasu ta hanyar gyara wasu 'yan kura-kurai ko ƙarin bayani. Harwayau babu wani shafi a duniya baki ɗaya da ya tattara ilimi da bayanai a yanar gizo a yanzu kamar wikipidiya, kuma miliyoyin ɗalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga manhajar a kullum.