Yaƙin Duniya na II
From Wikipedia, the free encyclopedia
Yaƙin Duniya na 2 da turanci World War II akan kintse rubutun kamar haka WWII ko WW2, har wayau ana ƙiran shi da turanci Second World War. Yaƙin duniya dai wani yaƙine da duniya baki ɗaya suka afka a ciki wanda ya kwashi tsawon shekaru shida (6) ana gwabzawa, tun daga shekara ta alif 1939 har zuwa shekara ta alif 1945. Mafiya yawan ƙasashen duniya tare da ƙasashe masu ƙarfi su ne suka ja daga a tsakanin su, inda suke yaƙan juna: Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda aƙalla mutane sama da miliyan ɗari ne (100,000,000) suka tsunduma a ciki daga kasashe sama da talatin (30). Mafiya yawan ƙasashen da suka shiga cikin yaƙin sun saka dukkan tattalin arzikin su, da kuma Masana'antunsu da ilimin su na kimiyya da fasaha don ganin sun yi galaba a yaƙin. Yaƙin duniya na II shi ne yaki mafi muni a duniya wanda Dan Adam bai taba gani ba, inda aka samu rasa rayukan mutane daga miliyan 50 zuwa miliyan 85, yawan cinsu fararen kaya ne daga Ƙasar Soviet Union wato Rasha a yanzu da kuma Kasar Sin. An kuma sami kashe-kashe, kisan kiyashi akan Yahudawa, tsarin jefa bama-bamai, mutuwa sanadiyyar yunwa da cututtuka, da kuma amfani da makaman kare-dangi a yaƙin Atomic Weapeons.
Ansoma yaƙin ne daga rana ga watan Satumba, shekara ta alif 1939 zuwa ranar 2 ga watan Satumba, shekara ta alif 1945 tsawon shekaru (6 da kwana daya 1)
- Yankin da yaƙin yayi kamari; Nahiyar turai, Pacific, Atlantic, Kudu maso gabashin Asiya, Sin, Gabas ta tsakiya, Mediterranean, Arewacin Afirka, da Tunkun Afirka, Australiya, North da South America
- Sakamako
Ƙasashen ƙawance Allied Countries sunyi nasara, an kifar da Gwamnatin Nazi dake Jamus, An samu faɗuwar Daulolin yankin Japan dana Italiya, Anfara amfani da Makaman kare dangi wato Atomic weapons, Inganta ayyuka da jiragen sama, rusa kungiyar League of Nations, ƙirƙirar Majalisar Dinkin Duniya wato United Nations, Fara ƙiyayya tsakanin Kasar Amurka da Rasha, fara yaƙin mummuƙe wato Cold war. Jagororin ƙungiyar ƙawance na Kasa da kasa,