Blaise Compaoré
From Wikipedia, the free encyclopedia
Blaise Compaoré (an haife shi ranar uku ga watan Fabrairu a shekarar 1951) [1] [2] ɗan siyasan Burkinabé ne wanda ya kasance shugaban kasar Burkina Faso daga shekarar, 1987 zuwa 2014. Ya kuma kasance babban abokin tafiyar Shugaba Thomas Sankara a shekarun 1980, kuma a watan Oktoban shekara ta, 1987, ya jagoranci juyin mulkin da a lokacin aka kashe Thomas Sankara. Babban abokin sa ne kuma amininsa. Daga baya, ya bullo da manufar "gyara", tare da jujjuya manufofin gwamnatin sa domin su hadu da na Duniya Wanda Sankara ke bi. Ya ci zabe a shekara ta, 1991, 1998, 2005, da 2010 a cikin abin da ake ganin rashin adalci yunƙurinsa na yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima don tsawaita wa'adin mulkinsa na shekaru 27 ya haifar da tashin hankalin Burkinabé na shekara ta, 2014. A ranar 31 ga watan Oktoba shekara ta, 2014, Compaoré ya yi murabus, inda ya tsere zuwa kasar Ivory Coast .
Blaise Compaoré | |||||
---|---|---|---|---|---|
8 ga Yuni, 1998 - 12 ga Yuli, 1999 ← Robert Mugabe - Abdelaziz Bouteflika →
15 Oktoba 1987 - 31 Oktoba 2014 ← Thomas Sankara - Yacouba Isaac Zida → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Ouagadougou, 3 ga Faburairu, 1951 (73 shekaru) | ||||
ƙasa |
Republic of Upper Volta (en) Burkina Faso Ivory Coast | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Chantal Compaoré (en) | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Mooré Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da statesperson (en) | ||||
Kyaututtuka | |||||
Mamba | Académie des sciences d'outre-mer (en) | ||||
Aikin soja | |||||
Digiri | captain (en) | ||||
Ya faɗaci | First Liberian Civil War (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Katolika | ||||
Jam'iyar siyasa |
Congress for Democracy and Progress (en) Union of Burkinabé Communists (en) Organization for Popular Democracy – Labour Movement (en) | ||||
IMDb | nm11200182 |