Fankasau
Abincin Hausawa / From Wikipedia, the free encyclopedia
Fankasau ko funkaso abincin hausawa ne da'ake yin shi da Alkama ko fulawa, ana kwaba garin alkama sai a sa shi ya kumbura, sai a soya. Ana cin fankasau ne da miyan taushe ko miyar dage-dage. Mafi yawanci anayin funkaso ne a lokacin hidimar sallah ko wani biki, saboda tsadar alkama da kuma hidimar yinsa.