Gerónimo Rulli
From Wikipedia, the free encyclopedia
Gerónimo Rulli[1] an haife shi a ranar 20 ga Mayu 1992) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Argentina wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida na ƙungiyar Eredivisie Ajax da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina.[2]
Gerónimo Rulli | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | La Plata (en) , 20 Mayu 1992 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Argentina | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Yaren Sifen | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai tsaran raga | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 1 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 84 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 189 cm |
Rulli ya koma kungiyar matasan Estudiantes a shekarar 2009, inda ya fara buga musu wasa a shekarar 2013. Daga tsakanin 2014 zuwa 2020, ya buga wa Real Sociedad wasa, sau biyu a matsayin aro kafin ya koma kungiyar ta dindindin a shekarar 2017. Ya buga wa Sociedad wasanni 170 a cikin shekaru biyar. Ya koma kulob din Montpellier na Faransa a matsayin aro a shekarar 2019. A cikin 2020, ya koma Villareal ya ci gaba da zama a kulob din na tsawon shekaru 2 da rabi, inda ya lashe gasar UEFA Europa League a cikin 2020-21.[3]
Rulli ya fito don Argentina a gasar Olympics ta 2016 a Brazil. A cikin Mayu 2017, ya sami kiransa na farko don tawagar ƙasar Argentina. Ya buga wasansa na farko na duniya a cikin 2018 da Guatemala a wasan sada zumunci da ci 3-0. Ko da yake bai buga ko wanne mintuna ba, Rulli ya kasance memba a cikin tawagar Argentina da ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022.[4]