Tony Elumelu
From Wikipedia, the free encyclopedia
Tony Onyemaechi Elumelu (An haife shine a 22 ga watan Maris a shekarar ta alif dari tara da sittin da uku miladiyya 1963) Shi dai wani masanin tattalin arziki ne, kuma dan-kasuwa, san nan kuma mai son taimakon jama’a ne, mazauni kuma haifaffen dan Afrika . Shine shugaban Heirs Holdings, The United Bank for Africa, Transcorp sannan kuma shine wanda ya kirkiro wata kungiya ta taimakon kananan yan kasuwa a Afrika wacce ake kira da The Tony Elumelu Foundation. Elumelu yanada shedan girmamawa ta The Nigerian National Honours, The Commander of the Order of the Niger (CON) kuma mamba ne a Order of the Fideral Republic (MFR) a shekarar ta 2003. Ya samu shaidan kasancewa mai hazaka a shekarar ta 2019 daga Nigeria’s National Productivity Order.
Tony Elumelu | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Anthony Onyemaechi Elumelu | ||
Haihuwa | Jos, 22 ga Maris, 1963 (61 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Makarantar Kasuwanci ta Harvard. Jami'ar Lagos Jami'ar Harvard Jami'ar Ambrose Alli | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki, Ma'aikacin banki da philanthropist (en) | ||
Mahalarcin
|
Elumelu yana cikin mutane dari (100) masu matukar amfani da aka lissafa a cikin mujallar lokuta (Time Magazine) a shekarar ta 2020.