Zazzabin Rawaya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Zazzabin typhoid, shine akafi sani da typhoid, cuta ce da kwayoyin cutar Salmonella serotype Typhi ke haifarwa. Alamun sun bambanta daga wanda ze fara mai sauki zuwa mai tsanani, kuma yawanci suna farawa kwanaki shida zuwa 30 bayan kamuwa da kwayar cutar. [1] [2] Sau da yawa a hankali a hankali zazzaɓi mai tsanani yakan tashi bayan wasu kwanaki da yawa. [1] Amma a wanna lokacin, yakan zo ne tare da rauni, ciwon ciki, cushewar ciki, ciwon kai, da amai marar tsanani. [2] [3] A Wasu mutane yakanzo masu da kurajen fata tare da tabo a jiki . [4] A lokuta masu yawa, mutane na iya samun rudani. [5] Idan ba'a yi magani ba, cutar na iya wuce makonni ko watanni. [4] Zawo na iya zama mai tsanani, amma ba a cika samun hakan ba. [5] Wasu mutane na iya zama ɗauke da kwayar cutar ba tare da ta saka su rashin lapiya ba , amma har kuma suna iya yada cutar ma wasu. Zazzabin Typhoid nau'in zazzabi ne na ciki, tare da zazzabin paratyphoid . [6] An yi imanin S. enterica Typhi tana sa rashin lapiya ne a cikin mutane kawai.
Zazzabin Rawaya | |
---|---|
Description (en) | |
Iri |
primary bacterial infectious disease (en) , anthroponotic disease (en) cuta |
Specialty (en) | infectious diseases (en) |
Sanadi | Salmonella enterica (en) |
Symptoms and signs (en) |
continuous fever (en) , Rashin karfi, ciwon kai, constipation (en) , rash (en) , bradycardia (en) , pallor (en) , gastrointestinal bleeding (en) , intestinal perforation (en) , insomnia (en) , abdominal distention (en) , confusion of consciousness (en) , delusion (en) , hepatomegaly (en) , Sifa, prostration (en) , gudawa leukopenia (en) |
Physical examination (en) |
physical examination (en) , complete blood count (en) , Widal test (en) , ELISEA (en) , microbiological culture (en) polymerase chain reaction (en) |
Medical treatment (en) | |
Magani | ciprofloxacin (en) , DL-ofloxacin (en) , pefloxacin (en) , azithromycin (en) , cefixime (en) , amoxicillin (en) , ceftriaxone (en) , cefotaxime (en) , ampicillin (en) , aztreonam (en) , imipen (en) , gatifloxacin (en) da levofloxacin (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10-CM | A01.0 da A01.00 |
ICD-9-CM | 002.0 |
ICD-10 | A01.001.0 |
ICD-9 | 002002 |
DiseasesDB | 27829 |
MedlinePlus | 001332 |
eMedicine | 001332 |
MeSH | D014435 |
Disease Ontology ID | DOID:13258 |
Ana samun cutar Typhoid ta hanyar kwayar cutar Salmonella enterica subsp. enterica serovar Typhi, wadda take girma a cikin hanji, peyers faci, mesenteric lymph nodes, saifa, hanta, gallbladder, kasusuwa da jini . [9] [10] tyhoid tana yaduwa ne ta hanyar ci ko shan abinci ko ruwan da ya gurbace da najasar mai kwayar cutar. [11] Abubuwan da zasu iya saka ka samu cutar sun haɗa da karancin samun tsaftataccen ruwan sha da rashin tsafta . [12] Wadanda har yanzu ba su kamu da cutar ba kuma suka ci gurbacewar ruwan sha ko abinci sun fi fuskantar hadarin kamuwa da alamun cutar. [10] Mutane ne kawai za su iya kamuwa da cutar; babu sanannun dabbobi da zasu iya kamuwa. [11]Anayin binciken ganeta ne ta hanyar shuka kwayoyin cutar daga samfurin marar lapiya ko kuma gano garkuwar jiki wadanda jiki ya samar ta dalilin cutar.[13][14][15] . Bada jimaw ba, sabbin manhajojin daukar bayanai da kuma yin bincike suna ba masu bincike damar kirkiro wasu sabbin hanyoyin gano cutar. Wannan ya hada da sauyawar kwayoyin dake cikin jini wadan da zasu iya nuna kwayar cutar typhoid.[16]
Na'urorin bincike a wuraren da typhoid ta zama ruwan dare sunada karanci sannan kuma ingancinsu a wurin bincike yayi karanci, yawan lokacinda ake bukata wurin bincike, karuwar yaduwar jurewar magungunan kwayoyin cuta, da kuma tsadar awo, suna daga cikin wahalaolin da ake samu inda babu isassun kayan aiki da ma'aikata na kula da lafiya.[17]
Alurar rigakafin typhoid na iya hana kusan kashi 40 zuwa 90% na lokuta a cikin shekaru biyu na farko. [18] Maganin na iya yin ɗan tasiri har zuwa shekaru bakwai. [19] Ga waɗanda ke cikin hadari ko kuma mutanen da ke tafiya zuwa wuraren da cutar ta zama ruwan dare, ana ba da shawarar yin rigakafi. [20] Sauran kokarin da ake na rigakafin cutar sun hada da samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli da kuma wanke hannu . [21] [22] Har sai an tabbatar da cewa mutum ya warke, mai cutar bai kamata ya shirya abinci ga wasu ba. [21] Ana yin maganin taifot da maganin kamar azithromycin, fluoroquinolones, ko cephalosporins na ƙarni na uku . [23] kwayar cutar typhoid tana bijirewa magunguna , wanda ya sa maganinta yaketa kara wahala. [23] [24] [25] A cikin 2015, an sami sabbin cututtukan typhoid miliyan 12.5. [26] Cutar ta fi kamari a Indiya. [27] tafi shafar yara. [27] [28] Typhoid ya ragu a kasashen da suka ci gaba a cikin 1940s sakamakon ingantacciyar tsafta da kuma amfani da maganin rigakafi. [28]. A kowace shekara ana ba da rahoton cutar kusan 400 a Amurka kuma an kiyasta mutane 6,000 suna da taifot. [29] [30] A cikin 2015, ya haifar da mutuwar kusan 149,000 a duk duniya - ƙasa daga 181,000 a 1990. [31] [32] Idan ba tare da magani ba, haɗarin mutuwa zai iya kaiwa kashi 20%. [33] Idan kuma anyi magani, yana iya kaiwa tsakanin 1% da 4%. [34] [33]. Typhus cuta ce daban. [35] Saboda irin alamun bayyanar su, ba a gane su a matsayin cututtuka daban-daban har zuwa 1800s. "Typhoid" na nufin "kamar typhus".[36].