Hanafiyya
Mazahabar hannafiya, daya daga cikin mazahabobi guda hudu na sunna / From Wikipedia, the free encyclopedia
Mazhabar Hanafiyya (larabci|حنفي) (Ḥanafī) tana daya daga cikin manyan Mazhabobi guda hudu wadanda addinin musulunci ke dasu, wurin karantar da Sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, Dan yin hukunce hukuncen (fiqhu).[1] ita ma dai Mazhabar ta samu sunanta ne daga sunan Babban Malaminta, wanda makarantarsa ce ake wa Mazhabar lakabi da shi, wato Alshaykh Imam Abū Ḥanīfa an-Nu‘man ibn Thābit, ya rasu a shekarar (d. 767),shi Tabi‘i ne, kuma dokokin akidarsa an samo su ne ta hanyar kiyayewar manyan Daliban sa da suka yi, Abu Yusuf da Muhammad al-Shaybani. Manyan Mazhabobin addinin musulunci daman da sune wadannan hudun da suka shahara, wato; Malikiyya, Shafi`iyya da Hanbaliya.[2][3].
Hanafiyya | |
---|---|
Mai kafa gindi | Imam Abu Hanifa |
Classification | |
Sunan asali | المذهب الحنفي |
Mazhabar Hanafiyya ita ce Mazhabar da ke da mafi yawan mabiya a tsakanin musulmai masu bin Sunnah a duk fadin duniya.[4] ita ce ake bi a kasashen da suka taba kasancewa karkashin mulkin daular usmaniyya (Ottoman Empire), da daular Mughal da masarautun shugabannin Turkic da ke Indian subcontinent, northwest China da Central Asia. A yanzu ana bin Mazhabar Hanafiyya a kasashe da yankuna kamar: Turkiya, da Balkans, Syria, Lebanon, Jordan, Palestine, Misra, wasu bangaren kasashen Iraki da Iran, bangaren Rasha, Turkmenistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, Uzbekistan, Afghanistan, Pakistan, bangaren Indiya da China, da Bangladesh.[4][5][6]