Masallacin Annabi
From Wikipedia, the free encyclopedia
Masallacin Annabi (Larabci ألمسجذ النبوي Al-Masjid An-Nabawi) Masallaci ne a birnin Madina na kasar Saudiyya, wanda Annabi Muhammad (S.A.W) ya kafa ginin shi, kuma shine mallaci na uku da aka gina a tarihi. Yana kuma ɗaya daga cikin masallatai da sukafi girma a duniya. Shine kuma waje mafi tsarki na biyu a Musulunci bayan masallacin Harami (ka'aba) dake birnin Makka na kasar ta Saudi Arabiya. Masallacin koda yaushe a bude yake domin aiwatar da aiyukan bauta ga musulmai.
Masallacin Annabi | |
---|---|
المسجد النبوي | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya |
Province of Saudi Arabia (en) | Medina Province (en) |
Babban birni | Madinah |
Coordinates | 24°28′06″N 39°36′39″E |
History and use | |
Foundation stone laying ceremony | 622 |
Addini | Musulunci |
Suna | Muhammad |
Maximum capacity (en) | 600,000 |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Tsawo | 105 m |
Parts | Hasumiya: 10 |
|
Asalin wajen shine gidan Annabi (s.a.w) , anan ya zauna bayan yayi hijira daga maka zuwa birnin na Madina a shekarar 623 Miladiyya. Shine kuma ya assasa gina shi. Asalin masallacin budadden gini ne. Masallacin ya kasance waje ne na rayuwar al'uma kuma wajen Shari'a sannan kuma Makaranta ta koyar da addinin Musulunci. Asannu a hankali sarakunan musulunci ne sukai ta kokari wajen fadada shi da kara masa gyara har yakai kyakkyawa kamar yadda yake a yanzu. Shine waje na farko a yankin larabawa da aka fara sakama hasken wutar lantarki. Masallacin na karkashin hukumar dake kula da masallatai biyu masu tsarki ta kasar Saudiyya. Masallacin yana a tsakiyar birnin Madina, akwai manyan Hotel-hotel da tsofaffin kasuwanni a kewaye da shi. Babban waje ne na aiwatar da aikin umara ga mahajjata da masu ziyarar Umara.
Bayan fadada shi ne da daular Umaiya tayi karkashin sarkin daular Kalifa Al-Walid I, sai ya hado harda makwancin sa (S.A.W) da wasu Sahabbai nasa guda biyi (kalifofin Khulafa'hur-Rashidun na farko da na biyu). Daya daga cikin manyan sanannun gurare a masallacin shine babbar koyariyar Hasumiya wadda ananne daidai dakin Ummuna Ai'sha (matar Annabi (s.a w). A ranar 19 ga watan Maris ne hukumomi a kasar Saudiyya suka bayyana sanarwar rufe kofofin masallacin tare da hana yin dukkan wasu aiyuka na ibada da taruwar jama'a sakamakon kamari da annobar cutar Covid-19 tayi ma duniya.[1]