Mikiya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Mikiya: ana kiranta da turanci da (Eagle) wata tsuntsuwa ce daga cikin tsuntsaye masu cin nama, sai dai wasu na gani kalmar Mikiya suna ne da ya haɗa baki ɗayan sunayen tsuntsaye masu cin naman junan su da kuma sauran dabbobi, suna kama da junan su. A taƙaice mikiya tsuntsuwa ce da take tashi sama kamar shaho itama kamar yadda shaho yake farauta haka take, sai dai ita tafi shaho hatsari don kuwa har naman mutane tana ci, musamman ƙananan yara. Akwai karin magana da hausawa keyi wai shi "Dirar Mikiya" wato anzo ba tare da an sanar ba. [1][2][3]
Mikiya | |
---|---|
Scientific classification | |
Kingdom | Animalia |
Phylum | Chordata |
Class | Aves |
Order | Accipitriformes (en) |
dangi | Accipitridae Vieillot, 1816
|
Kamar yadda nafaɗa ita Mikiya kusan tana da dangantaka da shaho da mujiya da sauransu. Masana sunce mafi yawa kaso sittin (60) na kalolin Mikiya ana samun sune a ƙasar Turawa da Afirka, bayan waɗannan yankuna ana samun kaloli daban-daban har guda 14 a Amerika da ƙasar Ostireliya. Ita Mikiya naman tsuntsaye take farauta don yin kalaci, ko da yake wani lokacin ma har mutane takan yi musu barazana musamman ƙananan yara, kamar yadda ya gaba ta.