Mohsen Fakhrizadeh
From Wikipedia, the free encyclopedia
Mohsen Fakhrizadeh Mahabadi ( Persian: محسن فخریزاده مهابادی Fa-Kh-Ree-Zadeh[1] 1958[2] – 27 November shekarar 2020) Cikakken dan kasar Iran ne masanin ilimin kimiyya da Physics. Ana masa inkiya da shugaban masana ilimin gudanar Nukiliya na kasar iran.
Mohsen Fakhrizadeh | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Qom, 1958 |
ƙasa |
Pahlavi Iran (en) Iran |
Harshen uwa | Farisawa |
Mutuwa | Absard (en) , 27 Nuwamba, 2020 |
Makwanci | Imamzadeh Saleh (en) |
Yanayin mutuwa | kisan kai (ballistic trauma (en) ) |
Karatu | |
Makaranta | Shahid Beheshti University (en) |
Harsuna | Farisawa |
Sana'a | |
Sana'a | nuclear physicist (en) |
Employers | Imam Hossein University (en) |
Kyaututtuka | |
Aikin soja | |
Fannin soja | Dakarun kare juyin juya halin Musulunci |
Digiri | brigadier general (en) |
Imani | |
Addini | Shi'a |
An haifeshi a birnin Qom a shekarar 1958, Fakhrizadeh ya shiga Rundunar kare juyin juya hali na musulunci na iran ( Islamic Revolutionary Guard Corps) bayan an tabbatar da tsarin Gwamatin Musulunci a 1979. Yayi karatu a Jami'ar Shahid Beheshti daga bisani kuma ya kammala karatunsa na Doktora a Jami'ar Isfahan. A farkon shekarar 1991 ya zama furofessa na physics a Jami'ar Imam Hossein.
Fakhrizadeh ya jagoranci kungiyar kariya tare da bincike wato Organization of Defensive Innovation and Research tare da wani aiki mai suna Green Salt Project domin inganta ma'adanan uranuyum, kaya masu fashewa da kuma kirkirar sabbin makamai da inganta su. Saboda nasarorin da fakhrizadeh ya samu a ayyukan da ake bashi, hakan yasa ya samu kyakykywan alaka da ayyukan gudanar da makamashin Nukiliya, a dalilin hakan kungiyar UN (United Nation), Kungiyoyin tsaro (Security Council) da kuma gamayyar Amurka suka daskarar da Kadarorin kasar iran a wurin shekarun 2000. A farkon shekarar 2010 ya fara wanzar da ayyukan daya ayyana zai gabatar na kungiyar da yake jagoranta wato kungiyar kariya tare da bincike Organization of Defensive Innovation and Research wanda su kuma Amurka sun kalli wannan yunkuri a matsayin Gudanar da makamashin Nukiliya tare da samar da makaman Nukiliya. Amma su kasar iran a gwamnatan ce ta musanta hakan. Shi kuma prime Minista na Isra'ela cewa yayi fakhrizadeh yaci gaba da aikin da kungiyar IAEA ta haramta wato na samarda makamashin Nukiliya wato AMAD Project . Bayan mutuwar Fakhrizadeh kasar ta girmama Fakhrizadeh inda ta bayyana irin gudunmuwwar daya bada wajen samar da rigakafi na Annobar korona tare da hanyotin magance ta.
A ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2020, k asar Isra'el ta kashe Mohsen Fajhrizadeh ta hanyar amfani da bindiga mai sarrafa kanta.[3][4] A watab Yunin shekara ta 2021 tsohon shugaban kungiyar leken Asiri ta Isra'el watao Mossad ya bayyana cewa sune suka kashe Fakhrizadeh[5]. Gwamnatin Kasar ta bayyana kisan Fahkrizadeh a matsayin mafi munin Ta'addanci[6], wannan kisan ya tada hankula sosai a yankuna kuma Zauren Dadtawa masu zartarwa a kasar sun tura takarda rufe wani bincike daga kungiyar IAEA akan gudanar da makamashin Nukiliya.