Muhammadu Bello
From Wikipedia, the free encyclopedia
Muhammed Bello (Larabci: محمد بلو) Shi ne sarki na biyu. Sarkin Musulmi[2] ya yi mulki daga shekara ta alif ɗari takwas da sha bakwai 1817A.c, har zuwa shekara ta alif ɗari takwas da talatin da bakwai 1837A.c. Ya kasance marubucin tarihi ne wanda kuma ke da Ilimin addinin Musulunci. Ɗan Usman Ɗan Fodio ne kuma mai masa hidima, wanda shine ya kafa Daular Sokoto kuma shi ne Sultan (Sarkin Musulmi) na farko. Lokacin mulkinsa, ya ƙarfafa da'awar yaɗa Musulunci a dukkanin yankunan Ƙasar Hausa, da tsarin karantar da mata da maza, da kuma kafa kotunan Musulunci, Ya rasu a watan Octobar, a ranar 25, shekarar alif ɗari takwas da talatin da bakwai, 1837, kaninsa Abu Bakar Atiku ne ya gaje shi, daga nan sai ɗansa mai suna Ali Babba bin Bello ya gaji sarautar a gurin Abubakar Atiku.
Muhammadu Bello | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Wurno, 1781 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Wurno, 1837 | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Usman Dan Fodiyo | ||
Yara |
view
| ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Muhammadu Bello | |
---|---|
Title | Sarkin Musulmi |
Personal | |
Haihuwa | 3 November 1781 |
Mutuwa |
25 October 1837 |
Addini | Islam[1] |
Iyaye |
|
Senior posting | |
Gada daga | Usman dan Fodio |
Magaji | Abu Bakr Atiku, Dan uwa |