Pep Guardiola
From Wikipedia, the free encyclopedia
Josep " Pep " Guardiola Sala, ( Catalan pronunciation: [ʒuˈzɛb ɡwəɾɗiˈɔlə] ; an haife shi 18 ga Janairu 1971), ƙwararren kocin ƙwallon ƙafa ne na kasar andalus kuma tsohon ɗan wasa, wanda shine yake kocin ƙungiyar kwallon kafan Premier League wato Manchester City a yanzu. Ana la'akari da yana daya daga cikin manyan manajoji na.kowane lokaci kuma yana riƙe da tarihin wasanni mafi yawa a jere da aka samu nasara a La Liga, Bundesliga da Premier League . [2]
Pep Guardiola | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Josep Guardiola Sala | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Santpedor (en) , 18 ga Janairu, 1971 (53 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ispaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Catalan (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifi | Valentí Guardiola | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifiya | Dolors Sala Carrió | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Abokiyar zama | Cristina Serra i Selvas (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ahali | Francesca Guardiola i Sala (en) da Pere Guardiola (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Yaren Sifen Catalan (en) Turanci Italiyanci Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 80 kg da 70 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 180 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Kyaututtuka | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm2150064 |
Guardiola dan wasan tsakiya ne mai matukar kwarewa wajen
bada gudunmuwada qoqari a qungiyarsa nci ya taka rawar gani sosiwasanni daya buga tare da qungiyarsasan . Ya shafe yawancin aikinsa tare da Barcelona, inda ya zama wani ɓangare na Kungiyar Mafarki na Johan Cruyff wanda ya lashe Kofin Turai na farko a 1992, da kofunan gasar Sipaniya guda huɗu a jere daga 1991 zuwa 1994. Ya taba zama kyaftin din kungiyar daga shekarar 1997 har zuwa lokacin da ya bar kungiyar a shekarar 2001. Bayan haka Guardiola ya buga wasa da Brescia da Roma a Italiya, Al-Ahli na Qatar, da Dorados de Sinaloa a Mexico. Ya buga wa tawagar kasar Sipaniya wasa sau 47 kuma ya bayyana a gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 1994, da kuma a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2000 . Ya kuma buga wasannin sada zumunci na Catalonia .
Bayan ya yi ritaya a matsayin dan wasa, Guardiola yazama mai horar da Barcelona B a takaice, wanda ya lashe taken Tercera División . Ya karbi ragamar horar da kungiyar farko ta Barcelona ne a shekarar 2008. A farkon kakarsa, ya jagoranci kungiyar ta Barcelona zuwa kan teburi na La Liga,da kuma nasarar lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, da kuma Copa del Rey, ya zama ƙaramin kocin daya lashe gasar Turai da aka ambata. A cikin shekarar 2011, bayan da ya jagoranci kungiyar zuwa wani La Liga da gasar cin kofin zakarun Turai sau biyu, Guardiola ya sami lambar yabo ta Majalisar Catalan ta Zinariya, lambar yabo mafi girma. A wannan shekarar, an kuma ba shi suna FIFA World Coach of the Year . Ya kawo karshen zamansa na shekaru hudu da Barcelona ne a shekarar 2012 tare da girmamawa 14, rikodin kulob .