Tanta
From Wikipedia, the free encyclopedia
Tanta ya kasan ce wani birni ne a cikin Misira, tare da yanki mafi girma na biyar a ƙasar, kuma yana da mazauna kimanin 658,798 kamar na 2018[1]. Tanta yana tsakanin Alkahira da Alexandria: kilomita 94 (58 mi) arewacin Alkahira da kuma kilomita 130 (81 mi) kudu maso gabashin Alexandria. Babban birnin Gharbia Governorate[2], cibiya ce ta masana'antar auduga[3]. Kuma daya daga cikin manyan titunan/layikun jirgin ƙasa ya ratsa ta garin Tanta[4][5]. Ana gudanar da bukukuwa na shekara-shekara a cikin garin Tanta na tsawon mako guda wanda zai fara daga ranar 11 ga watan Oktoba don murnar zagayowar ranar haihuwar Ahmad al-Badawi, wani adinin Sufaye na karni na 13, wanda ya kafa Badawiyya Tariqa a Misira kuma aka binne shi a Masallacin Ahmad Al-Badawi, babban masallacin Tanta. Tanta gari ne daya shahara wajen sayarda kayan makulashe (alawa) a shaguna da kuma gasasshen kaji[6].
Tanta | ||||
---|---|---|---|---|
طنطا (ar) | ||||
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Misra | |||
Governorate of Egypt (en) | Gharbia Governorate (en) | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 429,503 (2006) | |||
Labarin ƙasa | ||||
Altitude (en) | 12 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC+02:00 (en)
|